Player FM - Internet Radio Done Right
Checked 8d ago
nine 年前已添加!
内容由France Médias Monde and RFI Hausa提供。所有播客内容(包括剧集、图形和播客描述)均由 France Médias Monde and RFI Hausa 或其播客平台合作伙伴直接上传和提供。如果您认为有人在未经您许可的情况下使用您的受版权保护的作品,您可以按照此处概述的流程进行操作https://zh.player.fm/legal。
Player FM -播客应用
使用Player FM应用程序离线!
使用Player FM应用程序离线!
Al'adun Gargajiya
标记全部为未/已播放
Manage series 1219094
内容由France Médias Monde and RFI Hausa提供。所有播客内容(包括剧集、图形和播客描述)均由 France Médias Monde and RFI Hausa 或其播客平台合作伙伴直接上传和提供。如果您认为有人在未经您许可的情况下使用您的受版权保护的作品,您可以按照此处概述的流程进行操作https://zh.player.fm/legal。
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
25集单集
标记全部为未/已播放
Manage series 1219094
内容由France Médias Monde and RFI Hausa提供。所有播客内容(包括剧集、图形和播客描述)均由 France Médias Monde and RFI Hausa 或其播客平台合作伙伴直接上传和提供。如果您认为有人在未经您许可的情况下使用您的受版权保护的作品,您可以按照此处概述的流程进行操作https://zh.player.fm/legal。
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
25集单集
所有剧集
×Shirin ''al'adunmu na gado'' tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya leƙa jihar Adamawa ta yankin arewa maso gabashin Najeriya don duba yadda gwamnatin Jihar ta ƙara yawan Masarautu a wannan jiha tun cikin shekarar da ta gabata. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.…
Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi. A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al’adu ke kallon al’amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.…
Shirin Al’adunmu na gado na yau, ya yi duba ne kan al’adar shaƙe a ƙasar hausa da wasu kan yi a matsayin al’ada da kuma magani. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
A
Al'adun Gargajiya

Shirin Al’adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta jama’a baki daga ciki da waje. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........…
A
Al'adun Gargajiya

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ke kan al'adar shaɗi ko kuma Charo na sahun manyan al'adun ƙabilar fulani a ƙasashen Afrika ta yadda har sai wanda ya iya karɓaɓɓen shaɗi ke iya samun matar aure, yayinda a wasu lokutan ake gudanar da wannan al'adu a shagulgula don nishaɗi kuma jajirtacce shi ne jarumi.…
A
Al'adun Gargajiya

Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya. Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........…
Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al’adun duniya. Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al’adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa. Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........…
A
Al'adun Gargajiya

Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.
A
Al'adun Gargajiya

A yau shirin al’adun zai je jihar Nassarawa inda muka samu zantawa da mai Martaba Sarkin Nassarawa,daga bisani za mu je Jamhuriyar Nijar inda zamu duba koma bayan wakokin gargajiya a cikin al’umma.
Yau shekaru tara kenan da zama Sarkin masarautar keffi da mai martaba Dr alhaji shehu usman chindo yamusa,bayan rasuwar mahaifinsa mai martaba alhaji Chindo Yamusa na uku 3. A cikin shirin al'adu za ku ji tarihin Sarkin na Keffi.
Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma. A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya. Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....…
A
Al'adun Gargajiya

Shirin al'adunmu na gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gagarumin biki baje kolin al'adu a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya. An gudanar da bikin ne a fitacciyar cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery, wanda ya shahara a duniya, bikin ya tattaro mutane da dama daga sassan fasaha, kasuwanci, siyasa da diflomasiyya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aboulaye Issa........…
A
Al'adun Gargajiya

Shirin al'adunmu na gado tare da Aboulaye Issa, ya mayar da hankali ne kan al'adar gaɗa da ke ƙoƙarin gushewa tsakanin al'ummar Hausawa duk da tasirinta a shekarun baya musamman tsakanin matasa.
Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......…
欢迎使用Player FM
Player FM正在网上搜索高质量的播客,以便您现在享受。它是最好的播客应用程序,适用于安卓、iPhone和网络。注册以跨设备同步订阅。