Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI
Manage episode 444182723 series 1083810
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.......
23集单集